Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe, an haifi malam a garin Kuri a karamar hukumar Yamaltu Deba, a jihar Gombe.
Malam yayi makarantar firamare a garin Gombe, a islamiyya ta izala anan garin Gombe Sheikh kabiru Gombe ya samu haddar AL-QUR'ANI mai girma tare da gyara karatun sa a wajen malamai irin su : Sheikh Zarma Gombe, Da Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan. Ya kuma yi wasu karatunsa na ilimi a wajen maluma irin su Sheikh Usman Isah Taliyawa Gombe.
Sheikh Kabiru Gombe ya zama Alaramma mai jan baki a kungiyar izala tun yana karami, kafin daga bisani ya juya zuwa mai wa'azi wanda a halin yanzu duniyar Hausa take amfana da wa'azin sa.
Sheikh Kabiru Gombe bai tsaya iya wa'azi ba, yana taba kasuwanci sannan babban Manomi ne. Malam yana da mata hudu da yara da jikoki. Malam yana da baiwa kwarai, domin duk abun da malam ya haddace to da wuya kaga wannan abu ya salwanta a kwakwalwarsa.
Allah ya karawa rayuwar Sheikh albarka, ya bamu ikon aiki da abun da muke karantawa da wanda muke karantarwa. Amin.
Akwai sauran manhajjoji masu zuwa in saha Allahu da zasu kawo muku wadannan lakcoci :
Waye Mai Sallah - Sheikh Kabiru Gombe Mp3
ILLar Zina Kan Jama'a - Sheikh Kabiru Gombe
ILLar Shaye-Shaye - Sheikh Kabiru Gombe Mp3
Sunnah Sak Bidia Sam - Sheikh Kabiru Gombe
Illar Shi'a A Jiya - Sheikh Kabiru Gombe
Su Waye Masu Amana - Sheikh Kabir Gombe
Mutuwa Da Zaman Kabari -Sheikh Kabir Gombe
Riba da Illolinta - Sheikh Kabiru Gombe
Anfake Da Guzuma an Harbi Karsana - Gombe
What's new (v1.1)
- App now works on iPad and iPhone
- Supports iOS version 10.0 or newer
- Beautiful User Interface
Enjoy!